Wasu na ganin cewar mazajene kan sa mata irin wannan aiki na ta'addanci, wasu kuma sun dangantashi da cewa irin matan da ake satane ake sanyasu cikin wannan yanayi.
A Najariya ta’addanci irin ta kunar bakin wake musamman a arewacin Najeriya, abune na ban mamaki idan akayi dubi da irin zaman takewar yankin tun kaka da kakanni. Wani abin lura a tarihin kunar bakin wake na mata ya faro ne a jihar Gombe, sai jihar Kano, da kuma Bauchi, Neja, saikuma wanda ya faru shekaran jiya a garin Maiduguri jihar Borno.
Alhaji Yayale Ahmed, tsohon ministan tsaron Najeriya kuma dan takarar gwamnan a jihar Bauchi ya bayyana wannan yanayi da cewa, “wato idan tsarin zaman takewa na dan adam a garinsu ya tabarbare, ba mace bama kowaye zai iya shiga. Shi tsaron nan da kake gani kamar na jefa bom, mutum zai jefa bom ne ya kashe kansa saboda ya yarda da abin da zaiyi din, inba haka ba waye zai kashe kansa, kuma ka tunafa dan adam yafi dabba fa tsiya. Gurbacewar wannan abubuwa a gaskiya abune na takaici.”
Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad daga Bauchi.
Your browser doesn’t support HTML5