A karshen watan jiya ne kotun tsarin mulkin Janhuriyar Niger ta tabbatar da kasasncewar kujerar shugaban majalisar dokokin Niger Hama Ahmadou a matsayin kango, saboda haka ‘yan majalisun na da wa’adin tsawon kwanaki ukku tun daga lokacin da kotun ta fidda wannan hukunci don maye gurbin shugaban majalisar Hama Ahmadou dake cigaba da gudun hijira a kasar Faransa.
A sanyin safiyar yau dai ‘yan majalisun dokoki sun tapka muhawara mai zafin gaske a majalisar, Yayinda mai jan ragamar majalisa Malam Dauda Muhammadou Martai ya gabatar masu da sunayen masu bukatar kasanchewa kakakin majalisar, inda ‘yan adawa suka ce an ajiye takardun ba bisa ka’ida ba. Hakan ya janyo ‘yar hayaniya har ta Tsawon ‘yan mintoci a majalisar. Amma daga bisani, daya daga cikin ‘yan takarar dake bukatar kasasncewa kakakin majalisar Hajiya Hauwa Hambali, tace ta janye bukatar tsayawa takara a majalisar.
Ana cikin wannan rudani da rikici ne wasu ‘yan majalisun dokoki su 24 daga jam’iyyar adawa suka ajiye takardar bukatar tsige gwamnatin Birji Rafini saboda wasu dalilai da su ‘yan majalisar dokokin na adawa suka fada. Hakan kuma ya kara janyo wata muhawara da ta shafe wani dogon lokaci ana yin ta.
Yanzu haka dai takkadama na cigaba da kasancewa a zauren ‘yan majalisa, tsakanin ‘yan majalisun adawa da na masu rinjaye kan batun sake sabon kakakin majalisar dokokin janhuriyar Niger. Wani sabon batun shine ‘yan majalisun dokokin zasu sake tattaunawa don duba hanyoyin da suka cancanta don duba bukatar tsige firayin minista Birji Rafini da ‘yan adawar suka ajiye a yau.
Kamar yadda zaku ji a nan ga wakilin muryar Amurka Abdullahi Mamman Ahmadou da karin bayani.