WASHINGTON, D. C. - Asibitoci a larduna daban-daban da suka hada da gabashin Zhejiang da kudancin Jiangxi a cikin watanni biyu da suka gabata sun sanar da cewa za su rufe sassansu na haihuwa, kamar yadda sanarwar da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani ya nuna.
Asibitin Fifth People’s Hospital na birnin Ganzhou a Jiangxi ya fada a cikin shafinsa na WeChat cewa za a dakatar da ayyukan haihuwa daga ranar 11 ga Maris na bana.
Asibitin Magungunan Gargajiya na Jiangshan a Zhejiang ya sanar a shafinsa na WeChat cewa hidimarsu na masu haihuwa zai tsaya daga ranar 1 ga Fabrairu. Rufewar ya zo ne a daidai lokacin da masu tsara manufofin kasar China ke kokawa ganin yadda za a bunkasa sha'awar ma'aurata na haihuwa yayin da hukumomi ke fuskantar matsala mai girma na al'ummar da ta tsufa.
Yawan jama'ar kasar China ya ragu a shekara biyu a jere, a shekarar 2023 saboda rashin yawan haihuwa da kuma yawan mace-mace sakamakon COVID-19 ya kara saurin koma bayan da jami'ai ke fargabar zai yi babban tasiri na dogon lokaci kan ci gaban tattalin arzikin kasar.
Kiddidiga na baya-bayan nan da aka fitar daga hukumar lafiya ta kasar China sun nuna cewa adadin asibitocin haihuwa ya ragu zuwa 793 a shekarar 2021 daga 807 a shekarar 2020.
Kafofin yada labarai na cikin gida da suka hada da Daily Economic News sun ce raguwar jariran da ake haifa ya sa ba zai yiwu asibitoci da yawa su ci gaba da gudanar da ayyukansu na haihuwa ba.
"'Lokacin hunturu na haihuwa' da alama yana zuwa cikin sannu a hankali ne," in ji jaridar a ranar Juma'a.
Yawancin mata a kasar China sun zabi zama haka ba su haihu ba saboda tsadar kula da yara, rashin son yin aure ko dakatar da sana'o'insu a cikin al'ummar da take ta gargajiya inda har yanzu ake kallon su a matsayin manyan masu ba da kulawa, amma kuma ake ci gaba da nuna wariyar jinsi.
Hukumomi sun yi ƙoƙarin fitar da abubuwan ƙarfafawa da matakan haɓaka ƙimar haihuwa, gami da faɗaɗa hutun haihuwa, fa'idodin kuɗi da haraji da tallafin gidaje, don samun karin haihuwar yara.
Sai dai kasar China na daya daga cikin wurare mafi tsada a duniya wajen renon yara dangane da yawan kudin da ake samu ga kowane mutum, wata fitacciyar cibiyar nazarin kasar China ta bayyana a watan Fabrairu, yayin da ta yi cikakken bayani kan farashin abinda ake kashewa, da kuma lokaci da damar da akan ba matan da suka haihu.
Ana samun karin jarirai a asibitoci a fadin kasar China a cikin shekarar da suke kira Year of the Dragon, wadda ta fara a ranar 10 ga watan Fabrairu, kamar yadda wata kafar yada labarai ta kudi ta Yicai ta ruwaito, inda aka yi imanin cewa alamar ta zodiac a lokacin a kasar China na da matukar amfani. Amma masu binciken alƙaluman sun ce duk wani karuwar samun haihuwa na “jariri a lokacin shekarar Dragon” zai iya zama na ɗan gajeren lokaci ne.
-Reuters