Shugaban karamar hukumar Bulama, Muhammed Bulama, ya tabbatar da mutane 65 suka mutu kana wasu goma kuma suka jikata, kana ya ce yana gani wannan harin martani ne da Boko Haram ta kai bayan ‘yan kauyen sun kashe mayakanta 11 a makon da ya gabata.
A makon da ya gabata ne ‘yan Najeriya suka cika shekaru goma da fuskantar hare haren Boko Haram da suka hallaka sama da mutane dubu talatin suka fidda miliyoyin mutane a cikin gidajensu kana suka haddasa matsalar bukatar taimako a duniya.
Kungiyar Boko Haram ta yi fice wurin yin garkuwa ‘yan mata ‘yan makaranta da kuma sakawa matasa maza da mata bama bamai a jikinsu suna kai hare hare a kasuwanni da wuraren ibada da ma wurare masu cunkoson jama’a.
Kungiyar ‘yan ta’addan da take yada tsauraran ra’ayi da kuma kalubalantar ilimin nasara, ta musunta ikirarin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi cewa ta murkusheta. Rikicin Boko Haram dai ya shiga har kasashe masu makwabtaka da Najeriya da suka hada Nijer, Chadi da kuma Kamaru.