Yawan Karance-Karance Ya Sa Min Sha'awar Waka

Kabiru Yusuf Garba

Kabiru Yusuf Garba: Wanda aka fi sani da Kabiru Art - Mawakin rauji da wakoki na nanaye, mafi akasari ya kan yi wakoki da ake amfani da su a fina-finan Hausa, amma sai ya tsinci kansa cikin damuwa na yadda 'yan tada kayar baya suka yiwa yankin Arewa maso gabas cikas, hakan ya sa yaga kyautuwar waka ga marayun da rikicin ya ritsa da su.

Ya ce sakamakon ziyartar yankin a jihar Borno ne ya sa yaga ya dace ya kasa wakar gida-gida, domin fadakar da alumma sanin cewa bayan rikicin, yaya makomar wadannan yara, da aka kashe iyayensu.

Kasancewar sa mawaki mai tasowa sai ya nemi goyon bayan mawakiya Maryam Sangandale domin samar da wakar da zata daga marayun, da kuma gwamnatoci da su shigo cikin wannan al’amarain.

Yana me cewa a mafi yawan manyan titunan jihohin Arewacin kasar nan ne, marayu da dama ne suke yawo a matsayin al’amajirai domin neman taimako na abun kaiwa bakin salati.

Kabir ya ce dalilin da ya sa ya fara wakarsa shine, ya kasance mai yawan karance karance, ganin yadda maruba kan rubuta basirarsu a littafi shi ne yaga dacewar rera tasa basirar ta waka. Shi dai dan jarida ne baya ga nishadantarwa da ya ke yi.

Your browser doesn’t support HTML5

Yawan Karance-Karance Ya Sa Min Sha'awar Waka 5'10"