Shugaban hukumar ne James Comey ya bayyana haka a jiya Laraba, inda yace, a baya hukumar ta kan sami irin wannan yunkurin na Amurkawa sau 6 ko 8 ko ma sau 10 a wata a cikin shekarar 2014 da kuma cikin farkon shekarar 2015 data wuce.
To amma yace, tun daga nan kuma, baya wuce ma’aikatansu na FBI su kama mutum 1 a wata wanda yake kokarin fita daga kasar da irin wannan niyya ta zuwa Gabas ta Tsakiya don shiga cikin ‘yan ta’adda masu tsatstsauran ra’ayi.
Comey ya bayyanawa manema labarai cewa, babu ko shakka, wani abu ya faru na canzawar lamarin a karshe, musamman game da jan hankalin mafarkin ‘yan ISIS game da son jan ra’ayin Amurkawa.
To amma bai zurfafa bayanin yadda aka yi har yawan maniyyata shiga ISIS din ke raguwa ba. Amma yace ‘yan ta’addan na nan suna ci gaba da kokarin rinjayar mutanen dake da matsala a rayuwarsu.