Yaushe Za a Samu Wadatar Wutar Lantarki a Najeriya Bayan Makudan Kudaden Da Aka Kashe?

NEPA

Ba wani abin mamaki ba ne don an dauke wuta a Najeriya, amma abin mamaki ne wutar ta zauna a wuni, ko sa'o'i a yawancin sassan Najeriya.Tun daga manyan tashoshin wutar wato Kainji a jihar Neja ba ta wadatar da al'ummar yankin ba, kuma hakan yasa ba ta wadatar da sauran kasar ba.

Gwamnatin APC mai mulki a yanzu ta aza alhakin rashin ingancin wutar kan PDP da ta yi mulki tsawon shekaru 16. Daya daga tsoffin shugabanni a wancan karon har bugin kirji ya yi cewa ya kashe fiye da dala biliyan 15 kan samar da wutar, amma ina wutar, inji shugaba Buhari da ya ke nufin gwamnatin tsohon shugaba Obasanjo.

A labarin da jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa a tsawon shekaru 8 gwamnatin shugaba Buhari da ta tsohon shugaba Jonathsn sun kashe Naira tirilyan 1.164 kan samar da wutar, amma har yanzu ba a rabu da duhu ba.

A lokacin da wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya ya zanta da Ministar, ta ce za a iya samun wuta ta hanyar zuba jari na sassa masu zaman kan su don gwamnati ita kadai ba za ta iya wadatar da jama'a da wuta ba.

Shugaban hukumar raba wutar Usman Gur Muhammed, shima ya shaidawa Muryar Amurka irin nasarar da ya ce an cimma a lamarin wuta.

Ga dai cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: An Kashe Triliyoyin Naira Kan Samar Da Wutan Lantarki Tun 1999