Yau Za'a Ci Gaba Da Gwabzawa A Wasannin Europa League 2016/17

A Yayin da aka buga wasu wasanni a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai UCL 2016/2017, a matakin wasan zagaye na goma sha shida, jiya kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ta doke takwararta Napoli daci 3-1.

Bayern Munich, ta kasar Jamus ta lallasa Arsenal, ta kasar Ingila da kwallaye 5-1.

Za'a sake haduwa karo na biyu ranar Talata 7/3/2017, inda Arsenal, zata karbi bakuncin Bayern Munich, Arsenal dai tana neman kwallaye har hudu batare da an jefa mata ko daya ba kafin ta haye zagayen gaba ita kuwa Napoli zata barje gumi da Real Madrid, ne duk a ranar.

Napoli, tana bukatar zura kwallaye biyu da babu kafin zuwa matakin gaba, bayan haka kuma a yau za'a dawo cigaba da gasar cin kofin turai ta Europa League, 2016/2017 a zagaye na 32.

Kungiyar FK Krasnodar zata karbi bakuncin Fenerbahc da karfe 5:00pm, Celta Vigo da Shakhtar Donest, Borussia Monchenglabach, zata kara da Lyon sai Olympiakos da Osmanlispor, Athletico Bilbao zata kece raini da Apoel.

Sauran wasannin kuwa Villarreal zata barje gumi da Roma, Paok da Shalke 04 akwai Legia Warsaw da Ajax, Hopoel Be'er Sheva da Besiktas, Anderlecht zata gwabza da Zenit, daga karshe Manchester United, zata fafata da Saint Etienne.

Za'a buga wasanninne a lokuta daban daban agogon Najeriya Nijar Kamaru wanda ya kama tun daga karfe bakwai na maraice har zuwa tara na dare.