Bisa ga umurnin da shugaban majalisar koli a kan lamurran Musulunci a Najeriya, Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar, ya bayyana ranar Lahadi 7 ga Yuli 2024, ita ce 1 ga watan Muharram, watan farko a shekarar Musulunci, 1446 bayan Hijrah.
Bayan ga kasashen da ke amfani da tsarin watan Musulunci wurin tafiyar da ayyukkan gwamnati a duniya, sanin hakikanin kwanakin watan Musulunci ya kan zo da barkwanci ga jama'a a wasu kasashen.
Wasu al’umma da dama dai sun kasa bayyana kwanan watan kalandar Musulinci da aka tambaye su.
Wannan lamarin dai baya rasa nasa ba da yadda ma’aikata ke amfani da kalandar miladiya saboda da ita gwamnati take amfani a Najeriya tana biyan su albashi, shi yasa basa mai da hankali kan kalandar Musulinci.
To sai dai duk da haka wasu jama'a na ganin a Najeriya ana kan turba da za'a iya jawo hankulan mutane ga sanin kwanakin watannin Musulunci.
Da yake bayyana tasirin shekarar Musulunci ga Musulmin duniya, Dokta Ibrahim Liman Sifawa, malami ne na addini kuma masanin yadda tsarin kwanakkin wata ke tafiya, ya ce a Musulnci mafi yawan ibada da bayanan da aka yi na lokuta a cikin al-Qurani duka ana yi ga wannan shekara.
Ya ce kamar Ramadan, Zakka, Hajji, da kuma Idi ana yin su shekara-shekara, saboda haka wannan shekarar ta ke da muhimmanci, don da ita ake ibada, ita aka san lissafi da ita ko da mu’ammala ko da an samu wani sabani a Musulin ce.
Shekarar 1445AH ta zo kuma ta wuce, sai dai 'yan Najeriya sun ce an fuskanci kalubale da yawa da ba'a fatar sake fuskantar makamantansu a wannan sabuwar Shekara.
An jima dai ana kiraye-kiraye ga mahukunta a Najeriya da su mayar da aiki ta amfani da watannin Musulunci ko da 'yan kasa zasu kara samun masaniya a kan yadda kwanakin ke tafiya.
Sai dai kawo yanzu hakan bai samu ba, duk da yake a makarantu da kafafen yada labarai na wasu jihohi suna gwama yin amfani da kwanan watan kalandar Musulunci da na miladiya a ayyukkan su na yau da kullum.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5