Rana ce da ake kiran jama’a su koyi yin hakuri da juna a harkokinsu na yau da kullum, albarkacin ranar da aka haifi jagoran gwagwarmayar samun ‘yancin kan kasar Indiya, Mahatma Gandhi.
A sakonsa domin wannan rana babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Antonio Guteres yace kullum Duniya za ta ci gaba da koyi da matsayin marigayi Mahatma Ghandi wajen yin anfani da zaman lafiya domin kawo sauyi a tsakanin al’umma baki daya. Yana mai cewa ta anfani da wannan hanya ce za’a kaucewa zubar da jini da tashin hankali a duniya.
Bikin na bana dai ya zo ne a lokacin da aka kada gangar Siyasa a Nigeria yanayin da kuma ke haifar da tsoro da tashin tashina sakamakon akidar ko a mutu ko A a yi rai da ‘yan siyasa ke nunawa juna.
Jama’a kan alakanta tashin tashinan da ake fuskanta a duniya, musanman a kasashe masu tasowa akan ‘yan siyasa. Masana na ganin lokaci ya yi Na yin karatun ta natsu ga ‘yan siyasa da magoya bayansu domin kaucewa hargitsi.
Dr Bashir Yankuzo wani mai sharhi ne akan harkokin yau da kullum a Nigeria wanda ya bayyana bukatar da ake akwai ga ‘yan siyasa suyi koyi da magabata irin su Sardaunan Sokoto domin kaucewa rikicin siyasa dake haifar da hasarar rayuka. Yace an rasa shugabanni masu hangen nesa kodayake ba wai yana watsi da duk shugabannin na yanzu ba ne. Yawancin ‘yan siyasar yanzu burinsu ne su ci zabe su karbi kudadensu su ci gaba da sharholiya ba tare da tabukawa al’ummarsa komai ba.
Bayan rikicin siyasa dake haddasa hasarar rayuka da dukiyoyi, har ilau yau rikicin kabilanci da addini na daya daga cikin tashe tashen hankulan da ya dabaibaye Nigeria shekara da shekaru Bako Benjamin shugaban kungiyar jukunawa a Nigeria yana fatan gwamnati da shugaban kasa za su taimaka wajen magance shi. Ya yi kira ga shugaba Buhari da ya nuna halin ba sani bas abo wajen hukunta duk wanda ya yi laifi.
Dubbai ko miliyoyin jama’a ne ke rasa rayukan su a duk shekara a sassa daban daban na duniya sakamkon tashe tashen hankula. Ana bukatar kawo karshen rigingimun cikin nasara.
A saurari rahoton Babangida Jibrin
Your browser doesn’t support HTML5
--