Ranar 19 ga watan Nuwanban kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin
Duniya ta ware domin fadakar da al’umma kan muhinmancin gidajen bahaya mai tsafta a tsakanin al’umma.
A cewar majalisar ta dinkin Duniya, kimanin mutane biliyan hudu da dubu dari biyu ne ke rayuwa ba tare da wuraren bahaya mai inganci da tsafta ba, inda mutane miliyan 673 ke bahaya a filin Allah.
A shekarar 2013 ne majalisar dinkin Duniya, a karkashin hukumar kula da gidajen bahaya ta Duniya, ta ware wannan rana domin fadakarwa, da kuma ilimantar da jama’a game da muhinmancin yin bahaya a gidajen bahaya, a maimakon a fili.
Kiyasin hukumar lafiya dai ya nuna cewar mutane kusan dubu dari hudu
ne ke mutuwa a duk rana sakamakon kamuwa da cututtuka masu nasaba da
gidajen bahaya marasa tsafta. Ita ma hukumar UNISEF ta ce kananan yara
na kamuwa da cututtuka da ke halaka su, sabili da rashin wuraren bahaya
masu tsafta a Dinuya.
A Najeriya, yayinda hukumomi suka tashi tsaye wajen fadakar da jama’a akan muhinmancin gidajen bahaya masu tsafta, wasu daga cikin jama’a sun shaida wa Muryar Amurka cewar dole ne hukumomi su dauki matakin ba sani
ba sabo wajen tilasta wa masu gidajen haya gina wadatattun gidajen bahaya.
Malam Sani dake zaman wani malamin tsafta, ya ce dole a dawo da aikin
duba gari kamar yadda a ka yi a baya, domin saka ido da tabbatar da tsafta a wuraren jama’a, daban daban.
Ga rahoto cikin sauti daga wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5