Yau Za a Fara Sauraron Muhawarar Tsige Trump

Bayan kwashe wuni guda ana tafka muhawara akan ka'idodin shari'ar tsige shugaban Amurka Donald Trump, majalisar dattawan Amurka za su gana a yau Laraba don sauraron muhawara a rana ta farko daga wasu ‘yan majalisar wakilai da ke neman a tsige Trump daga mukaminsa.

Kafin karfe biyu na safiyar yau Laraba, a Majalisar Dokokin Amurka, ‘yan majalisar dattawa sun kada kuri'ar amincewa da ka’idodin shari’ar tsige Trump da shugaban masu rinjaye, Mitch McConnell, ya gabatar inda aka sami kuri’u 53 daga ‘yan Republican yayin da ‘yan Democrat 47 kuma suka yi akasin haka.

Wannan kada kuri’ar na zuwa ne bayan wasu jerin muhawara da aka yi game da wasu gyare-gyare da tsirarun ‘yan Democrat a Majalisar suka gabatar, akan ko a nemi karin bayanai da shaidu daga wasu jami’an fadar White House, da a baya aka bukaci su bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai a lokacin binciken tsige shugaban, amma fadar White House ta hana su, ko a’a.