Yau Litinin Shugaban Faransa Zai Fara Ziyara A Nan Amurka

Shugaban Faransa Emmanuel Macron

Shugaban Faransa zai fara ziyara a nan Amurka yau inda yake neman ya shawo kan shugaban Amurka ya canza ransa akan janye sojojin Amurka daga Syria kana ya bar yarjejeniyar nukiliyar Iran yadda aka cimma da ci gaba da aiki

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, yana haramar zuwa Amurka domin ziyarar aiki, inda zai gana da mai masaukin sa shugaba Trump. Yana son ya shawo kan shugaban na Amurka ya ci gaba da barin sojojin Amurka a Syria, har sai an ga bayan 'yan ta'addan kungiyar ISIS.

Gabannin isowarsa a nan Washington DC yau Litinin, shugaba Macron ya gayawa tashar talabijin ta FOX a hira da suka yi a afadar shugaban na Faransa a birnin Paris cewa, "Tilas mu sake gina Syria bayan yakin. Saboda haka ne nake ganin rawar da Amurka zata taka tana da muhimmanci."

Ya kwatanta Amurka azaman "wacce da wuya a cimma zaman lafiya da tunutbar juna tsakanin kasashen duniya ba tareda da ita ba."

Shugaba Trump yace yana son ya janye sojojin amurka daga Syria nan bada jimawa ba.