A yau Litinin ne ake sa ran mahaukaciyar guguwar nan ta Irma zata rage karfi yayin da take ratsawa zuwa arewacin Florida ko kuma Kudancin Georgia a cewar cibiyar dake nazarin muguwar guguwa ta kasar Amurka.
WASHINGTON DC —
Duk da haka masu hasashen yanayi sun kashedi cewar ambaliya da guguwar da Irma ta haddasa a gabar tekun kudu masu gabashin Amurka na iya jawo barazana ga rayuwar bil adama da kuma tsananta hali da ake ciki.
Bugu da kari, cibiyar guguwar tace akwai yuwar ratsawar muguwar iskar nan ta tornadoe a arewa maso gabashin Florida da Kudu maso gabashin Georgia da kuma Carolina ta Kudu da yammacin yau Litinin.
Da daren jiya Lahadi ne guguwar Irma tayi tsananin hade da iska mai karfi dake juyawar kilomita 155 cikin awa guda.