Ziyarar Yarima Harry, Gimbiya Meghan A Najeriya

Ziyarar Yarima Harry da Megan

Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce da sanyin safiyar Juma’a Yarima Harry zai gana da Babban Hafsan Hafsoshin rundunar tsaron Najeriya, Janaral Christopher Gwabin Musa.

ABUJA, NIGERIA - Kakakin hedkwatar tsaron kasar Birgediya Janar Tukur Gusau ya ce ziyarar Yariman na da tarihi, domin kimanin watanni goma da suka gabata sojojin Najeriya da suka nakasa a fagen fama sun halarci wani bikin gasar motsa jiki na kasa da kasa da shi Yariman ya kirkiro a karo na farko kuma suka samo lambobin yabo.

Hakan ya sa ya ji dadi kuma ya yi alkawarin zai kawo masu ziyara har gida don ya gansu.

Yarima Harry da Megan a Najeriya

Janar Gusau ya ce shi kansa Yariman shi ma tsohon soja ne, don haka ya san me ake nufi da in aka ce soja ya sami rauni a fagen daga.

Bugu da kari ita ma mai dakinsa, Gimbiya Meghan wacce bakar fatar Amurka ce, ta sa an mata wani bincike da ya nuna asalin kakanninta daga Najeriya su ke.

Daga bisani dai Yariman zai je jihar Kaduna inda zai gana da nakassun sojojin da suka sami rauni kuma suke jinya a asibitin sojoji na 44 REFFERAL da ke Kadunan kuma zai gana da Gwamnan jihar.

Daga nan kuma zai koma Abuja inda za a dan shirya musu liyafar cin abinci, ya kuma wuce jihar Legas idan ya dawo kuma zai koma gida Birtaniya.

Ziyarar Harry da Megan Najeriya

Yarima Harry wanda da ne ga Sarki Charles na uku da Gimbiya Diana, tsohon soja ne da ya fafata har sau biyu a karo daban-daban a yakin Afghanistan, kuma mutum na biyar cikin jerin masu jiran gadon sarautar Birtaniya.

Bayan ya bar aikin soji, ya kirkiro da gasar wasannin motsa jiki a matakin kasa da kasa na sojojin da suka sami nakasa a fagen daga mai suna INVICTUS GAMES.

Masana tsaro irin su Wing commander Musa Isa Salman na ganin wannan ziyara na da muhimmanci sosai musamman kasancewarsa tsohon soja kuma ‘dan sarauta mai kwarjini da farin jini.

Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:

Your browser doesn’t support HTML5

Ziyarar Yarima Harry, Gimbiya Meghan A Najeriya.mp3