WASHINGTON, DC —
Wani rahoton hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya, ya nuna cewar mashaya taba sigari da wadanda ke shakar hayakin taba kimanin mutane miliyan 8 ke mutuwa a duk shekara, sakamakon kamuwa da cututtukan dake da alaka da shan tabar ko shakan hayakinta.
A wata tattaunawa da Dr. Shuaibu Ibrahim, wanda yake cewa shan taba na haifar da cututtuka iri daban-daban, kamar ciwon cansa da ke shafar huhun dan adam.
Wakilin sashen Hausa ya zagaya don ji daga bakin wasu wanda suke bayyana ra'ayoyinsu akan illar taba. Wasu ma na ganin cewar akwai bukatar rufe kamfanonin taba domin hana shanta.
Ga cikakken rahoton wakilinmu Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5