Da take jawabi, kwamishinar harkokin ruwa ta jihar Borno, ta bayyana cewa kamar yadda majalisar dinkin duniya ta ga ya kamata ta tsayar da wannan rana a matsayin ranar ruwa ta duniya, ba ana mayar da hankali kan ruwa kadai bane.
Tsabtace muhalli na daya daga cikin batutuwan da ake dubawa domin suna da alaka da lafiyar jama’a dan haka suna da alaka da ruwa. A misali, akwai al’ummomi da dama da basu da makewayi, kuma suna zubar da shara a duk inda suka ga dama, lamarin da ka iya gurbata ruwan sha, wanda babbar barazana ce ga lafiyar bil’adama.
Da take amsa tambayar da wakilin sashen Huasa na muryar Amurka ya yi mata akan kokarin da gwamnatin jihar Borno ke yi na wadata jama’ar jihar da ruwan sha mai tsabta, kwamishinar ta bayyana cewa yanzu haka gwamnatin jihar na kokarin kammala wata gagarumar madatsa da zata rika samar da akalla lita miliyan tara a kowace rana wanda ake sa ran kammalawa nan ba da dadewa ba.
Daga karshe ta yi Karin haske akan muhimmancin samun ruwa akalla lita shidda ga kowane dan adam a rana domin ya sha ya kuma yi wanka da kuma sauran wasu bukatu, koda shike akwai wurare da dama dake fama da karancin ruwa.
Ga cikakken rahoton Haruna Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5