Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Bankuna Sun Fara Tseguntawa Hukumomin Yaki Da Cin Hanci Kudaden Haramun


Jami’an bankunan Najeriya kamar yadda jaridar Thisday ta samo labari mai tushe, sun shiga sahun masu tseguntawa hukumomin yaki da cin hanci na Najeriya, kudin haramun da ‘yan zarmiya suka boye bankuna.

Ma’ajiyun suna dauke ne da sunayen ‘yan uwa ko yaran masu zarmiyar da kuma lambobin shedar ajiyar banki mai dauke da tambarin yatsun hannu, wanda za a iya amfani da su wajan gano asalin mai ajiyar.

Alhaji Garba Umar Yobe, tsohon babban jami’in banki ne, kuma ya bayyana cewa wannan matakin yana bisa doka, ya kuma kara da cewa yawancin asusun ajiyar ana fara sa masu kananan kudade ne, sai daga baya a fara aje miliyoyi, dan haka doka ta tanaji a bada rahotanni duk sati akan irin su.

Tun lokacin da aka kaddamar da shirin fallasa masu zarmiya ake samun makudan kudade, Su kuma masu tsegumin suna samun ladan matakin da suka dauka, kuma ‘yan siyasa da shugabannin al’umma na yabawa wanna a mataki da aka dauka.

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki Alhaji Inuwa Yahaya, ya bayyana farincikinsa akan wannan mataki da aka dauka akan wadanda ya kwatanta da kaska, mai makalewa jikin dabba tana shan jininta, wato barayin dukiyar Najeriya.

Mai taimakawa shugaban kasa kan labaru Shehu Garba, ya ce ma’aikatan banki sun taka rawa wajan fallasa irin wadannan kudade, sai dai wasu kan bukaci a raba biyu a basu kashi guda wanda hakan bai dace ba domin dukiyar kasa ce, amma dokar ta bada hurumin a ba duk wanda ya kawo irin wadannan bayanai wani kaso daga ciki.

Ga cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya daga Auja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG