Hanyar sadarwar radiyo ta zama kafa da bata da na biyu wajen saurin isar da sako zuwa sako sako da lungunan duniya musamman a kasashe masu tasowa inda ba'a faye samun wutar lantarki kodayaushe ba.
Ministan wasanni da matasa na Najeriya Solomon Dalung na cikin 'yan Najeriya dake sauraren labarun radiyo kullum.
Barrister Dalung yace radiyo ya taka rawa kwarai wajen taimakawa talakawa ta gane 'yancinsu. Wajen girka dimokradiya radiyo yayi taimako. Haka ma wajen kiwon lafiya da aika sakonni da sada zumunci tsakanin al'umma.
Ga kuma wani misali na sauraren radiyo da shugaba Buhari ya bayar a jajiberen zaben 2015. Yace a radiyon Muryar Amurka ya ji wani na cewa zai sayar da katin zabensa domin ya sayi buhunan masara ma gidansa su ci. Wasu mata ma sun ce zasu sayarda katunansu saboda talauci.
Shugaban kungiyar muryar talakawa Zaidu Bala Kofa Sabuwa na ganin cancantar shagali a wannan ranar saboda, injishi radiyo ya zama tamkar makaranta.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5