12 ga watan Agusta, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yin dubi kan irin halin da matasa ke ciki.
WASHINGTON D.C. —
Abubuwan da akan duba sun hada da irin gudunmuwar da matasa ke bayarwa wajen ci gaban kasa da kuma irin kalubalen da su ke fuskanta a rayuwa, musamman wadanda su ke zama masu cikas wajen cimma burinsu.
Taken wannan sheraka ta 2016 shi ne “Hanyar kai wa ga muradun 2030: Kawar da talauci da tabbatar da dorewar hanyoyin masu amfani da samar da ababan rayuwa.”
A ranar 17 ga watan Disambar 1999 Majalisar Dinkijn Duniya ta amince da kebe wannan rana ta matasa.
A Najeriya, wakilinmu Muryar Amurka, Babangida Jibril, ya yi dubi kan wannan rana ga kuma rahoton da ya aiko mana daga Legas a kudu maso yammacin Najeriya:
Your browser doesn’t support HTML5