Taken ranar mata ta wannan shekarar kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar shi ne daidaito tsakanin jinsi kan samun aiki, biyan albashi, samun ilimin zamani da sakar musu da mukaman gwamnati kamar yadda aka sakar wa maza.
Madam Ibrahim Uminni Mumminuna daraktar sashen dake kula da tsarin jinsi a ma'aikatar kyautata rayuwar mata da yara a Jamhuriyar Nijar ta ce daidaito da ake fadi tsakanin maza da mata ba ana nufin cewa maza da mata daya suke ba amma bisa fannin aiki daya da su keyi to a biyasu alabashi daidai kada na maza ya fi na mata.
Dangane da dalilin da ya sa har yanzu mata basu ga an yi daidaito ba tsakaninsu da maza a fannin aiki , ilimi da mukaman gwamnati, Malam Mumminuna na ganin jahici ne na mutane ya janyo haka. Injita ko addinin Musulunci ya gargadi mata da su nemi sana'ar yi ba su zauna haka ba basu da abun dogaro ga kai. Malaman addini sun taimaka masu da hadisai inda aka ce mace ta nemi ilimi.
Daga jamhuriyar Nijar zuwa tarayyar Najeriya mata sun kuduri anniyar maida hankali wajen wayewa mata kawuna domin wannan rana tasu ta yi tasiri. Daga yanzu zasu shiga karkara suna ilimantar da matan akan hakkinsu da abubuwanda yakamat su tashi su yi ba wai sai matan bariki ba. Zasu sa wakilai a duk gundumomi da zasu dinga zagayawa suna fadakar da mata.
Ita ko shugabar Gidauniyar Khalum wato Khaltum Muhammad kungiyarta ta tashi haikan ta yaki fyade da sace yara mata da ake yi a arewa maso gabas. A cewarta sace 'yan matan Dapchi ya mayar da hannun agogo baya domin akwai wasu 'yan matan da suka ce makarantar boko ta fita kansu. Dole su tashi su fadakar da mutane.
A sakon daya gabatar dangane da ranar ta mata ta wannan shekarar babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antoni Guterres ya ce samun daidaito tsakanin jinsi sai da iko sabili da haka ne majalisar ta shi ta karfafa mata domin su ma su samu ikon fada a ji da ikon aiwatar da abubuwan kansu da ikon dogaro ga kai.
Ga karin bayani daga wadannan rahotanni uku
Rahoton Tamar Abari daga Jamhuriyar Nija
Your browser doesn’t support HTML5
Rahoton Haruna Dauda daga Bornon Najeriya
Your browser doesn’t support HTML5
Sai kuma rahoton Abdulwahab daga Bauchin Najeriya
Your browser doesn’t support HTML5