Yau Ce Ranar Koyawa Matasa Dogaro Da Kai

Matasa a wajen hawan Sallah a Kano

15 ga watan Yulin kowace shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin bita da nuna muhimmancin koyawa matasa dogaro da kai.

Wannan kuma damace ta kawar da tunanin matasan daga shiga munanan dabi’u da zaman kashe wando.

Matsalar ayyukan yi a tsakanin matasa na daga cikin manyan abubuwan da ke sa matsa su baude a Najeriya, inda sukan shiga hanyoyin shaye-shaye da sace-sace ko kuma hadaka dai kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Matsalar yin garkuwa da mutane da satan shanu na daga cikin matsalolin da rashin ayyukan yi kan haifar

A wata hira da ya yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka, Dr Bawa Abdullahi Wase, ya ce rashin aikin da masana’antu fama da shi a yankin arewacin Najeriya, na daga cikin ababan da suka haddasa matsalar satan shanu a yankin.

Domin jin karin bayani kan muhimmancin wannan rana wacce aka yi mata take a wannan shekara da “koyar da sana’oi domin samarwa matasa abin yi.” Saurari rahoton da Babangida Jibril ya aiko mana daga Legas:

Your browser doesn’t support HTML5

Yau Ce Ranar Koyawa Matasa Dogaro Da Kai - 3'13"