Cibiyar Kulawa da Iyali ‘Center For Family Initiative’ ta gudanar da wani taro a unguwar Kubwa dake birnin Abuja, don nuna bukatar fahimtar juna tsakanin magidanta da matansu musamman ma a kasashe masu tasowa dake fuskantar radadin tattalin arziki.
Shugabar kungiyar Princess Osita-Oleribe, ta ‘karfafa yaki da cin zarafin mata da yara, haka kuma da yaki da fyade da ke neman zama ruwan dare game duniya. Wani abu da kungiyoyin kan tabo ya hada da yadda yara ko masu rukon yara kan ganawa yaran azaba da sunan horo ko don kin jininsu.
Haka nan kungiyar ta tabo batun dorawa yara ayyukan kwadago da suka fi karfinsu da kuma kalubalen shan miyagun kwayoyi.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5