Malam Mustapha Baba Illela wani malamin addinin Islama ya bayyana ma'anar hijabi yana mai cewar hijabi kalma ce ta Larabci kuma tana nufin tsari, tsarin kuma, tsare mace.
Yace umurni ne na Allah cewa mace tayi lullubi ta yadda ba zata nuna wani bangaren jikinta ba da zai kawo sha'awar maza. Yace matan Manzon Allah (SWA) da matan sahabansa suna lullube jikinsu duk lokacin da zasu fita. Mace ba zata sa tufafin da zai nuna jikinta ba ko ya nuna suffar jikinta kamar gabobi da ka iya motsa sha'awar maza. Tufan da zata sa ya zama mai fadi ba mai kama jiki ba da zai rufe duk jikinta baicin fuska da hannayenta.
Hajiya Fatuma Amiru Muhammad wadda ta jagoranci bikin ranar hijabin ta yi karin haske. Tace da ba'a gane menene hijabi ba amma yanzu duk duniya ta sani cewa hijabi na cikin dokar musulunci dalili ke nan aka sa daya ga watan Fabrariru duk duniya a fito a nuna mahimmancin lullubi na hijabi
Uwargidan gwamnan jihar Bauchi Hajiya Abubakar tace ba'a bukatar wata doka domin yin anfani da hijabi saboda Allah ya riga ya bada umurni akan sanya hijabi. Iyakacin abun da za'a yi shi ne a bi dokar da Allah ya bayar.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5