Yau ce ranar bikin cika ciki a nan Amurka

Talotalo ake bikin cika ciki a nan Amurka

Yau Amurkawa a duk fadin kasar ke bikin cika ciki wanda ya samo asali tu lokacin da turawan farko suka shigo kasar inda suka yi bikin cika ciki domin godewa Allah ya basu sabuwar kasa kuma sun yi bikin da talotalo ne kuma har yanzu haka ake yi

Yau Alhamis Amurkawa za su yi bikin Cika-Ciki , da ake cewa Thanks Giving da turanci, kamar yadda su ka saba – wanda ya hada da haduwa da ‘yan’uwa da abokai a ci abinci, da kallon farati da kwallon kafa da sauransu; ga wasu kuwa lokaci ne na hutu da fara yin sayayya musamman na Kirisimeti.

To amma shagalin, a wannan shekara ta 2017, da kuma shaharren bukin nan na paratin Macy Thanksgiving da akan yi a unguwar Manhattan na birnin New York, zai kasance ne cikin matsanacin matakan tsaro.

Faratin, wanda kan janyo ‘yan kallo wajen 200,000, na zuwa ne ‘yan makonni kawai bayan da aka zargi wani dan asalin kasar Uzbekistan da amfani da wata motar daukar kaya da ya yi hayarta wajen bin kan mutane a hanyar masu hawa keke, inda ya kashe mutane 8.

Wannan buki na cika ciki na zuwa da al’adu iri-iri; wanda daga cikinsu shi ne tafiya a hadu da ‘yan’uwa na jini da abokai. Ana kiyasin mutane miliyan 49 ne za su yi tafiye-tafiye gabanin wannan hutun, wanda hakan ya dara na bara da miliyan guda; don haka ya zama bukin cika ciki mafi armashi cikin kusan shekara 10.