Akwai kuma shirin ganawa da Steffan de Mistura zai yi da wakilan jami’iyar adawa a yau Alhamis, wuni guda bayan yace bai ga wata alama da nuna za’a cimma nasarar warware rikicin ba, amma sai yanayin siyasa na wannan lokaci na nuna yuwuwar samun zaman lafiya.
Bangarori masu yaki da juna na Syria sun gana da juna a birnin Geneva kimanin watanni tara a can baya. Tattaunawarsu ta sake warware dalilin sake barkewar rikici bayan yarjejeniyar tsagaita wuta.
De Mistura ya amince cewar nasarar sake komawa ga tattaunawa da bata yi tasiri a baya ba, zata ta’allaka ne ga hada kan bangarorin wurin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wutar ta yanzu.
Yace Rasha da ta tsara yarjejeniyar tare da Turkiya a Astana babban birnin Kazakhstan, tana amfani da karfin fada nata wurin ganin an yi aiki da shirin tsagaita wuta.
De Mistura ya kara da cewar ya yi kira ga sauran kasashe da suke fada ‘yan adawar su ji, da su gargadesu su yi aiki da shirin tsagaita wutar kuma su daina takalar waccan bangare.