Yau Ake Zaben 'Yan Majalisa Da Gwamnoni a Amurka

  • Ibrahim Garba

Masu zabe a Amurka

Kallo ya koma Amurka, inda manyan jam'iyyun kasar wato da Republican (Rifofilikan) mai mulki da Democrat (Dimokarat) babbar jam'iyyar adawa, ke fafatawa a zaben gwamnoni da majalisa na rabin wa'adi.

Kamar yadda akasari aka sani, Amurka babbar kasa ce kuma mai matukar karfin tattalin arziki da soji. Don haka ta na da tasiri matuka a siyasa da tattalin arziki da kuma zamantakewar duniya baki daya. Hasali ma, ita ce ta fi bayar da gudunmowa da zarar an samu wani bala’i a wani bangare na duniya. Saboda haka, abin da ya shafi Amurka kusan ya shafi kowa a duniya - au kai tsaye, au a fakaice.

To yau dai ake wasu muhimman zabuka a Amurka na rabin wa’adi, wato da zaben gwamnonin jahohi da na ‘Yan Majalisar Dattawa da ‘Yan Majalisar Wakilai.

Amurka dai na da manyan jam’iyyun siyasa biyu: wato da jam’iyyar masu ra’ayin rikau ko Republican (Rifofilikan) da kuma jam’iyyar masu ra’ayin sassauci ko Democrat (Dimokarat).

Akwai jimlar kujeru 535 a majalisar dokokin tarayyar Amurka. Majalisar Dattawa na da kujeru 100, a yayin da kuma Majalisar Wakiliai ke da kujeru 435.

Bayan wannan zaben manufofin harkokin wajen Amurka za su ta’allaka ne kan irin jam’iyyar da ta yi rinjaye a majalisun dokokin tarayyar nan biyu.