Yaron Jirgi Na Son Komawa Gida Ne

Mahaifiyar ba-Amurken nan dan asalin kasar Somaliya da ya gudu ta wajen shiga mazaunin tayar jirgin saman da ya gitta bisa Pacific ta e dan nata yana so ne ya isa wurinta a Afirka.
Matar mai suna Ubah Mohammed Abdullah ta ce ta kadu sosai da halin da dan na ta ya shiga da kuma yadda har ya dau wannan kasadar ga rayuwarsa.

A wata hirar da Sahin Somaliyanci na Muryar Amurka ya yi da ita, Ubah ta ce dan na ta, mai suna Yahya Abdi, ya ji kwanan nan cewa ta na da rai, bayan kuwa a baya ubansa ya gaya ma ta cewa ai ta mutu.

Masu binciken a Amurka sun ce shi wannan dan shekaru 16 vda haihuwar ya kutsa cikin filin jirgin Sama na San Jose, da ke jihar California, sannan ya hau kafar tayar jirgin sama ya isa har mazaunin tayar a karkasin jirgin mallakin wani kamfanin Hawaii.

Masu binciken sun ce ya yi sanar rayuwa duk kuwa da karancin iskar oxigin da kuma tsananin sanyi a yayin tafiyar tsawon sa'o'i sama da biyar zuwa Hawaii, inda aka kama shi sannan aka kai shi asibiti.

Ubah, wadda ke zama a sansanin 'yan gudun hijira da ke gabashin Ethiopia, ta ce ta yi kuka kuma ran ta ya baci yayin da ta ji halin da danta ya shiga. Ta ce mutane da yawa a sansanin sun karfafa mata gwiwa.