Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Isra’ila Da Hezbollah Na Iya Rugujewa

Lebanon Israel

Sabunta hare-haren roka da mayakan Hezbullah suke yi a Lebanon, da kuma hare-haren ramuwar gayya da Isra'ila ke kai wa, su na kara matsin lamba kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta ‘yan kwanaki da aka cimma, da nufin kwantar da tarzoma a yankin da ke fama da rikici.

Da yammacin ranar Litinin dakarun tsaron Isra'ila suka kai wasu hare-hare a fadin kasar Lebanon, inda suka zargi kungiyar Hezbullah da ke samun goyon bayan Iran da bijirewa yarjejeniyar ta hanyar kai wa Isra'ila hari da rokoki.

Isra'ila ta ce hare-haren da take kaiwa sun hada da auna dimbin cibiyoyin harba makaman roka na Hezbollah, da mayakan 'yan ta'adda da sauran cibiyoyin aikin kungiyar ta Hezbullah.

A yammacin ranar Litinin, ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta ce hare-haren da Isra'ila ta kai a garuruwan Haris da Talousa sun kashe mutane tara tare da jikkata wasu uku.

Tun da farko kuma ma'aikatar ta ce wasu hare-haren Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon sun kashe wasu mutane biyu.

Rikicin ya biyo bayan harin roka da kungiyar Hezbollah ta kai kan wani sansanin sojin Isra'ila a yankin gonakin Shebaa da ake takaddama a kansa, wanda Hezbollah ta bayyana a matsayin "harin gargadi na tsaro."