Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis ya ce babu wata shawara da Amurka ta yanke akan janye hannunta a yarjejenira shirin Nukiliyar Iran ta shekarar 2015, amma Amurka tana aiki da kawayenta na Turai domin ganin ko akwai abin da za a yi domin inganta yarjejeniyar.
Ya bayyana cewa Amurka ta gane cewa, yarjejeniyar bata da wani tasiri akan makamai.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, wanda ya kammala ziyara a Amurka cikin makon nan ya bayyana cewa, yayi imanin shugaban Amurka Donald Trump, zai fidda Amurka daga cikin yarjejeniyar.
An ba Shugaba Trump, zuwa ranar 15 ga watan Mayu, ya tsayar da shawara akan ko zai sake kakaba wani takunkumin tattalin arziki da kasar ta cire akan Iran, a nata bangaren kuma ta amince da daina ayyukanka na Nukiliya.