Kwamitin kula da harkokin waje na majalisun dokokin Amurka, sun amince da wata doka jiya Talata, kan duk wani shawara da aka cimma kan tattaunawar nukiliya da Iran, ta zamanto ‘yan majalisa sun duba ta domin amincewa da ita ko rashin amincewa.
‘Yan kwamatin dai sun kada kuri’a inda aka samu amincewar ‘yan kwamitin baki ‘daya, yanzu haka wannan doka zata tafi zuwa majalisun kasar biyu domin dubata. Fadar shugaban kasa dai na ganin shugaba Obama ka iya rattaba hannu kan wannna doka.
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da takunkumin karya tattalin arziki ga shugabannin kungiyar Shi’ite na Yamen da kungiyar ‘yan tawaye ta Houthi, kuma sun bukaci kungiyoyin da su fice daga babban birnin Sana’a da duk garuruwan da ‘yan tawaye suka kame.
‘Yan majalisar dai sun kada kuri’a inda baki ‘daya suka amince a jiya Talata.
Wakilin Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin yace, wannan kira bai da alaka da kawo karshen haren haren sama da Saudiya ke jagoranta kan ‘yan tawayen ba, wadanda suke fafatawa domin taimakawa kasar Yemen, wadda kasashen duniya na marawa shugaban kasar Abd-Rabbu Mansour Hadi baya.