Dabi'ar yi wa mata fyade wani ciwo ne da ke barin tabo mai wuyar bacewa. Bisa la'akari da abubuwan da ke faruwa ga mata da suka tsinci kansu cikin wannan hali, dalili kenan da Majalisar Dinkin Duniya taga dacewar kebe 19 ga watan Yuni domin tattaunawa akan wannan al'amari mai mutukar daurin kai.
Kare 'yanci da hakkokin yaran da aka haifa ta hanyar fyaden da akayi a lokutan tashe tashen hankula shine taken ranar ta bana, dalili kenan da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, a sakon sa yazo da wasu misalai na irin wadannan matsaloli.
Yaran da aka haifa a lokutan tashin hankali kan tsinci kansu cikin halin rashin takardun zama 'yan kasa, sannan ba wuya su tsinci kansu cikin kungiyoyin tsageru shekaru goma kachal bayan haihuwarsu, yayin da a wani lokacin su da mahaifan su ake musu kallon masu goyon bayan kungiyoyin tada kayar baya.
Majalisar Dinkin Duniya ta hanyar sakatare janar dinta ta bayyana cewa a shirye take ta hada kai da gwamnatoci da sarakunan gargajiya da na addinai da kungiyoyin fararen hula domin bullo da matakan wannan matsala tun abun bai wuce intaha ba.
Your browser doesn’t support HTML5