Yara 10 Cikin 100 Ne Ke Iya Karatu Da Harshensu Na Asali - USAID

Yemi Osibanjo Ya Ziyarci Sabuwar Makarantar Kwana Da Aka Ginawa Marayu A Borno

Cibiyar raya kasa da kasa ta Amurka wato USAID, ta gudanar da wani bincike kan ilmin yara a fannin iya karatu da harshensu na asali.

Binciken ya gano cewa, yara 'yan makarantar firamare kasa da 10 cikin 100 ne a jihar Bauchi suke iya karatun haruffa da harshen Hausa.

Sannan binciken ya gano cewa a jihar Sokoto kuwa, kashi biyu ne kacal cikin 100 ke iya karatun.

A dangane da hakan ne hukumar ta USAID ta zabi wasu cibiyoyin ilmi a jihohin biyu domin shawo kan matsalar.

USAID

A jihar Bauchi, an zabi kwalejin ilmi ta Adamu Tafawa Balewa domin gudanar da shirin da za a horas da malamai kan dabarun koyar wa wanda za su je su koyawa malaman makarantun firamare sabbin hanyoyin koyar da yaran.

Jami’in koyar da sabbin dabarun koyar da yaran firamare da ke gudana a kwalejin Adamu Tafawa Balewa, Malam Aminu Shu’aibu Baba, ya yi karin bayani kan shirin da ake fatan zai samar da yanayin da zai inganta ilmin yaran firamare a jihar Bauchi.

Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammed Kauran Bauchi, ya ce akwai matakan da gwamnati ke dauka dangane da yadda za’a inganta matsayin ilmi a jihar.

Saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Jihar Bauchi.

Your browser doesn’t support HTML5

Yara 10 Cikin 100 Ne Ke Iya Karatu Da Harshensu Na Asali - USAID