'Yar Tseren Mata Na Mita 100 Ta Kai Wasan Karshe A Gasar Olympics

Tobiloba Amusan

Tobiloba Amusan ‘yar Najeriya za ta yi wasan karshen na tseren mata na mita100 da ake tsallake shingaye a wasannin Olympic a birnin Tokyo na kasar Japan a ranarLitinin, bayan da ta samu gurbin shiga wasan karshen a yau Lahadi.

Amusan ‘yar shekaru 24 ta yi nasarar zuwa wasan gaba ne bayan nasara da ta yi a wasan kusa da na karshe na daya a filin wasa na Tokyo Olympic, inda ta kamala tsrene cikin dakiku 12.62 kana ‘yar kasar Bahamas Devynne Charlton tana biye da da ita a matsayi na biyu da dakiku 12.66.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya fada cewa Amusan zata yi tseren na gobe Litinin ne a kan layi na 6 tare da wadanda su kuma suka yi fice zuwa wasan karshen.

Tana da tarihi na kamala tseren cikin dakiku 12.48 da ya kai ta ga zama ta hudu a fannin wasan a duniya.

Amusan itace ta hudu a duniya a wannan tseren mat ana tsallaka shingaye kana itace ta biyu a wasan karshe na gobe Litinin da ‘yann wasa 8 zasu fafata.

Zakarar duniya na wannan wasa Kendra Harrison, ba-Amurkiyar nan, itace fitacciya a wasan goben.