'Yar Najeriya Ta Rasu daga Ebola

Gwamnatin Jihar Legas ta karyata jita-jitar da ke yaduwa mai cewa Likitan nan da ta kamu da cutar zazzabin Ebola ta rasu.

A taron manema labarai da kwamishinan kiwon lafiyan Jihar Legas yayi, Dr. Jide Idris yace babu gaskiya game da batun mutuwar likita.

Amma Dr. Idris ya bayanna cewa likitan na kebabben wuri da ake mata magani, kuma tana tare da sauran ma’aikatan kiwon lafiyan da suka kamu da cutar.

Dr. Nasir Sani Gwarzo, shine shugaban yaki da cutar a Najeriya “likitan bata rasu ba, tana nan ana yi mata jinya, amma mai kula da marasa lafiya daya ta rasu”.

Wannan cuta dai ta bullo ne a kasar Guinea, inda a halin yanzu ta dauki rayukan mutane sun kusa 1,000 a duk fadin yammacin Afirka.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yar Najeriya Ta Rasu Daga Ebola - 2'53"