Kungiyar Vital Voices mai zaman kanta, wadda ke aiki da shugabannin mata don karawa mata kwarin gwiwar fitowa a dama da su a fannoni da suka hada da tattalin arziki da shiga harkokin siyasa da kuma kare hakkin mata. ita ce ta zabi mata hudu a fadin duniya domin karramasu kan muhimmiyar gudunmawar da suke baiwa al'umma.
Daya daga cikin matan da wannan kungiya ta zama itace Habiba Ali, daga jihar Kaduna, wadda ta kirkiri wani kamfani dake taimakawa al'umma wajen kare muhalli, ta hanyar samar da na'urori masu amfani da hasken rana da suka hada da murhun girki, wanda mutane za su rika dafa abinci ba tare da amfani da itatuwan bishiyoyi ba.
An gudanar da bikin girmama matan ne a fitatciyar cibiyar tunawa da tsohon shugaban Amurka John F. Kennedy, cikin manyan bakin da suka halarci bikin akwai tsohuwar 'yar takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton da kakakin Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi dama sauran wasu jiga-jigan Amurka.
Habiba Ali shugabar kamfanin Sosai Renewable Energy, ta yi murna kwarai da gaske da irin wannan karramawar da ta samu, wadda bata taba tunanin a iya tsawon rayuwarta za ta taba ganin irin wannna rana ba.
Domin karin bayani saurari hirar Habiba Ali Da Abdoulaziz Adili Toro.
Your browser doesn’t support HTML5