An gudanar da binciken ne akan ayyuka da dama da aka yi tsakanin shekarar 2007 da 2015.
Daga cikin batutuwan da ake zargin mutanen sun yi rub da ciki dasu akwai shinkafar da kasar Japan ta tallafawa kasar Nijar da ita. Sai kuma wasu makudan miliyoyin sefa da aka yi tanadi domin biyan kauyawan da ayyukan gina madatsan ruwan Kan Daji suka shafa.
Akwai kuma wata badakalar kudaden wani asibiti dake birnin Yamai da dai sauransu.
Sakatare Janar na kungiyar yaki da cin hanci da rashawa Mamman Wada ya yaba da yunkurin tare da nuna bukatar hukumomi suyi adalci. Yace abun da suke so shi ne yin aiki da dokokin kasa, 'yan kasa su zama daya. Tunda aka fara wannan to a cigaba kada a fasa. Kada a yi son rai ko son kai.
Sabanin yadda aka saba gani can baya a wannan lokacin hukumomin sun shimfida sharuda ga wadanda aka cafken su soma mayar da kudaden da suka wawura kafin su sami kansu.
Ila Kani na 'yan jarida masu ganin an yi komi a bayyane yayi murna da matakin. Yace da idan an cafke wadanda suka wawure kudin gwamnatin sai a kaisu gidan kaso inda suke zuwa su zama sarakuna. Idan yanzu ana amshe abun da suka sata kowa zai shiga hankalinsa.
Saidai sakatare janar na kungiyar Transparency na cewa kwace kudade kadai ba zai yi maganin masu handame kudaden jama'a ba sai idan an hada da gurfanar dasu gaban kuliya domin matakin hukumci ya biyo baya.
Ya zuwa yanzu bincike na cigaba da rutsawa da wasu mutanen da sannu a hankali sunayensu ke bayyana a jerin mutanen da ake zargi kuma a cewar wata majiyar gwamnati matakin zai cigaba har sai an zakulo duk wadanda suke da hannu a almundahanan da aka tafka a zamanin gwamnatocin da suka shude har zuwa lokacin gwamnatin dake ci a yau da zummar mayar wa kasa dukiyarta da aka wawure.
Souley Mummuni Barma nada karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5