'Yansandan Najeriya Basu da Ikon Hana 'Yan Shiya Yin Muzahara - Musa

Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky shugaban kungiyar Shiya a Najeriya

Abdullahi Muhammad Musa sakataren sashen dalibai na kungiyar shiya yace 'yansandan Najeriya basu da ikon hana kungiyarsu yin muzahara saboda babu dokar kasa da tace sai an nemi izinin yin gangami ko wani taro daga 'yansandan.

Inji Abdullahi 'yansandan dai sun hana ne domin basa bukatar a yi muzaharar ta kowane hali, dalili ke nan da suka yi anfani da karfinsu suka hana.

Akan ko su 'yan shiya basa tsoron mutuwa idan lokacin muzahararsu suka fada cikin rikicin da har ya kaiga mutuwa sai Abdullahi yace su addini su keyi kuma basa tsoron mutuwa. Yace shi wannan addinin da su keyi burinsu ne ma a kashesu a kanshi. Dole ne su yi addini koda ma za'a kashesu a kansa. Yace babu wani annabin musulunci da ya zo har yayi nasara ba'a kashe wasu nashi ba.

Suna yin muzahara ne akan dalilai biyu. Na farko shi ne su nuna wa gwamnati suna bukatar a sako masu jagoransu, wato Shaikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky. Na biyu kuma su al'umma su san gaskiyar abun da ya faru musamman a Zaria.

Yace yanzu mutane sun fara gane abun da ya faru domin daga farko sojoji sun yada wani bidiyo amma basu nuna yadda suka shiga mutanensu ba ko kuma yadda suka wuce ba. Bayanan da su keyi sun sa mutane suna gano ainihin abun da ya faru.

Abdullahi yace lokacin da yamutsin Zaria ya faru shi yana gidan jagoran nasu Shaikh El-Zakzaky a Gellesu. Sun ga duk abun da ya faru, yadda sojoji suka dinga kashe mutane har a gidan jagoran nasu.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yansandan Najeriya Basu da Ikon Hana 'Yan Shiya Muzahara - Musa