‘Yan sandan Birnin na Las Vegas sun ce Stephen Paddock mai shekaru 64, wanda ya fito daga yankin Mesquite a jihar Nevada dake nan Amurka, ya kai harin ne a kan dandazon jama’ar da yawansu ya kai dubu 22, a wani budadden wuri da ake taron wasannin waka, inda ya yi ta cullo harsashai daga dakin otel dinsa dake bene na 32 a otel din da ake kira Mandalay Bay.
Shugaban ‘yan sandan Birnin na Las Vegas, Joseph Lombardo, ya ce nan da nan aka tura gwanayen ‘yan sandan na SWAT, wandanda suka burma dakin maharin inda suka tarar da shi a mace.
A cewar Lombardo, sun yi ammanar cewa Paddock ya kashe kansa ne, yayin da aka tsinci akalla bindigogi 10 a dakin otel din nasa.
Sai dai shugaban ‘yan sandan bai bayyana wannan hari a matsayin na ta’addanci ba.
“Da farko sai mun gano mene ne dalilinsa na kai wannan hari, sannan idan akwai wasu dalilai da ke da nasaba da ta’addanci baya ga cewa akwai yiwuwar mutum ne da ke cikin halin kuncin rayuwar da yake so ya halaka mutane da dama, lokaci ne zai ba mu dama, kafin mu saka wannan hari a cikin wannan aji.”
A jiya Litinin, shugaban Amurka Donald Trump, ya kwatanta harin a matsayin “tsantsan rashin imani”, sannan ya yabawa ‘yan sanda Birnin na Las Vegas kan yadda suka yi gaggawan kai dauki.
“Ina so na mika godiya ta ga ‘yan sandan Birnin Las Vegas da duk sauran wadanda suka kai daukin farko, saboda irin jarumtakar da suka nuna wajen ceto rayukan jama’a da dama. Abin al’ajabi idan aka yi la’akkari da irin zafin naman da suka nuna wajen dakile salwantar karin rayuka. Yadda aka gano maharin cikin gaggawa bayan harbin farko da ya yi, wani abu ne da za mu ci gaba da nuna godiya akai. Hakan ya nuna tsantsar kwarewa.”
A halin da ake ci, ‘yan sandan Las Vegas, na kokarin fahimtar dalilin da ya sa Stephen Paddock ya kai wannan hari, wanda shi ne mafi muni a tarihin Amurka a wannan zamani.