'Yansandan Jamus Sun Cafke Wani Dan Asalin Siriya dake Kokarin Hada Bam

Jaber S. dana asalin Siriya da aka kama yau a Jamus

Yan sandan kasar Jamus sun ce watakila mutumin da aka kama yau litinin a kasar bisa zargin shirya kai hare-haren bam yana da alaka da kungiyar nan ta Daesh ko ISIS.

Babban jami'in 'yan sanda na yankin Saxon yace take-taken mutumin sun nuna alamun cewa yana da alaka da kungiyar Daesh.

Wasu 'yan kasar Syria su uku wadanda dan gudun hijirar Syria mai suna Jaber Al-Bakr mai shekaru 22 da haihuwa, ya nemi mafaka a wurinsu, sun gane shi, sai suka taru suka daure shi, suka kira 'yan sanda.

Jami'in 'yan sandan yace mutanen uku sun daure al-Bakr a cikin gidansu dake birnin Leipzig. Daya daga cikinsu ya kawo hoton al-Bakr zuwa wani caji ofis na 'yan sanda wadanda suka tabbatar shine, suka kuma je suka kama shi.

Jami'in yace a daure aka mika musu wannan mutumin.

Yan sanda sun fara neman Albakr ne bayan da suka samu daruruwan gram na wani sinadarin hada bam mai suna TATP a cikin gidansa dake Chemnitz. Wannan sinadarin shine tsagera suka yi amfani da shi a hare-haren Paris da Brussels.

Albakr dai ya kasance a Germany tun shekarar 2015, lokacin da aka tabbatar dashi a matsayin dan gudun hijira, Sannan ya taso ne daga wajajen Damascus dake Syria.