Kamfanin Dillancin Labarai na Turkiyya ya ruwaito cewa ‘yan sanda suna rike da wasu mutane shida, wadanda ake zargi suna da hanu a harin, wanda ya jikkata mutane 10
An dai cafke mutumin ne a garin Aksary mai tazarar kilomita 700 daga birnin Istanbul, yayin da ya ke tafiya a wata mota tare da wasu mutane biyu, inda aka same shi da wata takardar shaida ta bogi.
Babu dai wanda ya dauki alhakin wannan hari, kuma babu wanda ke cikin mawuyacin hali a cikin wadanda suka raunata daga harin.
Harin dai ya shafi wasu motoci ne da aka ajiye a kusa da ofishin ‘yan sandan, sannan tagogi da dama sun fashe a cewar Kamfanin Dillancin labaran kasar ta Turkiyya.
Kasar ta Turkiyya dai ta sha fama da hare-haren ta’addanci cikin shekarar nan, wadanda kungiyar IS da ta PKK ke yawan kaiwa.