Ranar Asabar goma ga wannan watan za'a gudanar da zaben gwamnan Edo wanda zai maye gurbin na yanzu da wa'adinsa ya kusa cika.
Baicin motocin sintiri dari biyar da hamsin babban sifeto Ibrahim Idris ya aika da mataimakin sifeto da wasu kwamishanonin 'yansanda
Kemfen tsakanin jam'iyyar APC mai mulki da PDP wadda ta sha kaye a zaben 2015 ya fi daukan hankali don PDP tayi shagube inda tace idan an zabi dan takarar APC Obaseki zai hada kai da Buhari wajen mayar da jihar mai bin shari'ar musulunci.
Nan take ofishin kemfen din Obaseki ya fito da sanarwar kore zargin da nuna cewa ai ma mahaifin Obasekin ya jagoranci kafa mijami'ar Katolika ta farko a birnin Benin.
Kwamitin riko na PDP ya tsayar da Iyamu a matsayin dan takara wanda kuma hukumar zabe ta amince dashi amma dan takaran bangaren Modu Sheriff na jiran hukuncin kotu.
Inuwa Bwala kakakin bangaren Modu Sheriff yace doka tace kada INEC ta karbi wani dan takara sai daga hannun Modu Sheriff.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5