Yanayi Mara Kyau Ya Sa Jirgin Attahiru Ya Sauka A Filin Jirage Na Kaduna – Hedkwatar Tsaro

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor (Twitter/@DefenceInfoNG)

Bayanai sun yi nuni da cewa kamata ya yi jirgin ya sauka a filin jirage na rundunar sojin saman kasar da ke Kaduna.

Yayin da hukumomin ke kokarin gano abin da ya haddasa hatsarin jirgin sama da ke dauke da babban hafsan sojin Najeriya, hedkwatar tsaron kasar ta ce rashin yana mai kyau ne ya tilastawa jirgin sauka a filin tashin jirage na Kaduna.

Attahiru ya rasu a ranar Juma’a tare da wasu sojoji 10 cikin har da janar-janar, a lokacin da jirginsu ya fadi a kusa da filin tashin jirage na kasa da kasa da ke Kaduna.

Bayanai sun yi nuni da cewa kamata ya yi jirgin ya sauka a filin jirage na rundunar sojin saman kasar da ke Kaduna.

“Wannan abin alhinin ya faru ne bayan da jirgin ya sauka a filin tashin jirage na kasa da kasa da ke Kaduna saboda rashin yanayi mai kyau.” Sanarwar da hedkwatar tsaron ta fitar dauke da sa hannun darektan yada labarai, Brig. Janar Onyema Nwachukwu ta ce.

Karin bayani akan: Kaduna​, Taraba, Ibrahim Attahiru, Nigeria, da Najeriya.

Hasashen da hukumar NiMet mai kula da yanayi ta yi a Najeriya a shafinta na Twitter, ya nuna cewa, a ranar Juma’a za a samu gajimarai masu duhu a wasu lokuta da kuma hasken rana a awannin safe a yankin arewacin kasar tana mai cewa, akwai kuma yiwuwar aukuwar tsawa a wasu sassan jihar Taraba.

Sanawar ta kuma mika sakon ta’aziyyarta, ga daukacin iyalan mamatan.

Hedkwatar tsaron ta Najeriya ta jaddada cewa za a kaddamar da bincike domin gano abin da ya haddasa faduwar jirgin wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna.

“Babban Hafsan tsaron kasa, Janar Lucky Irabor, ya ba da umurnin a kafa kwamitin bincike, domin gano musabbabin hatsarin.”

Rahotannin daga Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya na cewa tuni an yi jana’izar babban hafsan sojin kasar, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru a ranar Asabar, hade da wasu daga cikin sojojin da hatsarin ya rutsa da su.