Yanar Gizo Ta Janyowa Netflix Koma Baya A Najeriya

Shekaru da dama har yanzu kamfanin shirya fina finai na Nollywood a Najeriya ya dogara sosai da rarraba fim din da suke yin a gida.

Amma shekaru goma da suka gabata, masu shirya fina finai sun canza yadda suka yi inda suka maida hankali na ware kudade kadan, da suke samar da fina finai da yawa kuma masu inganci, wanda hakan ya sake samarwa da kamfani kima a idon duniya.

Sai dai kamfanin nuna fina finai na kebule, Netflix ya fara nuna fina finan da aka yi a Najeriya a sheakarar 2015, amma saboda rashin yanar gizo mai inganci da kuma tsadar siyan data ya hana kamfanin ya samu karbuwa na nuna fina finai a Najeriya.

Itama Happy Juliet, mai fitowa a fina finai da kuma ta ke shiryawa, ta shafe shekaru da dama a masana’antar. Sai dai ta ce tana amafani da kudi kadan wajan shirya fina finan ta kamar yadda ta ke yi a duk shekara don ta samu ta biya kudade kadan ga masu rarraba fina finai, a gida da kuma kaucewa rasa kudin shiga daga masu satar fasahar fina finai.