Daga wayoyin hannu zuwa motoci, talabijin, da firiji, dama sauran wasu na’urorin zamani da suke hade da yanar gizo, duk tsarin dake hada wadannan na’urorin ana kiran shi yanar gizon game gari “Internet of things” a turance.
Birnin Los Angels, gari na biyu mafi girma a kasar Amurka, wanda zirga-zirga kan iya zama wani abu mai wuya, saboda kasancewar cunkoso musamman idan aka hada da tafiya a mota.
Hakan yasa karamar hukumar birnin ta fito da wani sabon tsari, da zai taimaka wajen rage cunkoso, ganin yadda garin yake zagaye da yanar gizo a kowane bangare.
Idan aka duba wuta mai bada hannu a kan titi, na amfani da yanar gizo, mitocin biyan kudin ajiyar motoci, da yadda motoci ko wayoyin hannun mutane ke dauke da yanar gizo, yasa suke ganin za a iya inganta amfani da yanar gizon wadda mutun zai iya amfani da wayar sa, don sanin inane ake da wajen ajiyar mota da babu kowa, ta amfani da wata sabuwar manhaja da suka kirkira, haka zata sanarwa mutun a duk lokacin da fitila mai bada hannu zata tsayar da matafiyi.
Shi dai wannan sabon tsari, mutane zasu iya saukar da manhajar a wayar su, da bada izini ga manhajar data dauki bayanan inda suke don hadawa da sauran na’urori da suke kusa da mutum da kuma masu amfani da yanar gizo.