Taron ya biyo bayan wani faifan bidiyo da sakon murya da ‘yan bingigar suka fitar dake baiwa gwamnatin Najeriya wa’adin sakin ‘yan uwansu ko kuma rayuwar mutanen da suka yi garkuwa da su na cikin hadari.
Iyalan wadanda aka yi garkuwa da su suna dauke da kwalaye da ke nuna neman Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da masu ruwa da tsaki su yi abin da ya dace domin tseratar da iyalan nasu, suna mai cewa kada a dauki batun ‘yan bindigar a matsayin barazana.Aminu Lawal Othman na daya daga cikin iyalan wanda suke hannun ‘yan bidigar kuma ya halarci taron, ya ce ya kamata gwamnati ta tashi tsaye domin kubutar da iyalansu.
Hidayat Yusouf wadda ita ma ‘yan uwanta biyu mata na hannun ‘yan bingigar na ganin matakin da gwamnati ta ce tana dauka wajen ceto ‘yan uwan nasu yana tafiyar hawainiya.
Iyalan sun kuma yi kira ga gwamanti da kada hankalinta ya karkata kan harkokin siyasar 2023 da kasar ke tunkara.
Tun bayan harin hukumar sufurin jirgin kasar ta Najeriya b ata ayyana ranar dawo da zirga-zirgar jirgin na kasa daga Abuja zuwa Kaduna ba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hauwa Umar:
Your browser doesn’t support HTML5