'Yan Tawayen Taliban Sun ce Sun Kama Sassan Kunduz na Arewacin Afghanistan

Taliban

'Yan tawayen Taliban sun ce sun kama sassan garin Kunduz na arewacin Afghanistan, bayan da su ka kai wani samame da asuba daga bangarori daban-daban na birnin.

Kafafen yada labaran wurin sun ce mayakan sun kwace ginin Majalisar lardin, da wani asibiti mai gadaje wajen 200 da kuma wasu muhimman gine-gine.

Gidan talabijin na Afghanistan ya ba da rahoton fafatawa a harabar hedikwatar 'yansanda da kuma ofishin gwamnan lardin, sannan sun kuma kwace gidan yarin birnin su ka saki fursunoni.

Shaidu da kuma kungiyar ta Taliban sun ce an kafa farar tutar 'yan tawayen a babban dandalin birnin.

Jami'an gwamnatin Afghamnistan sun ce ana cigaba da gwabza fada a Kunduz, to amma ba su tabbatar da ikirarin Taliban na kwace muhimman gine-gine ba.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Cikin gida Sadiq Sadiqi ya shaida ma Muryar Amurka cewa jami'an tsaron kasa sun hallaka 'yan tawaye wajen 25, su ka ce babu wani sojin gwamnati da aka kashe. "'Yan tawaye da 'yanta'adda sun kai hari kan birnin daga sassan uku zuwa hudu." A cewar Sadiq.