Kungiyar hakkin bil adama adam ta Birtaniya dake da hedkwata a Birtaniya, wacce ta ke sa’ido akan yakin na Syria ta ce, Sojojin Turkiyya sun hada kai da 'Yan tawayen Syria domin aiwatar da harin na ranar Talata inda suka kwace yankin dake wajen yammacin Al-Bab.
Garin ya kasance mai matukar muhimmanci a yankin Arewacin Syria, wanda ya ke kara zama waje da ake yawan samun tashe tashen hankula.
Dakarun Syria sun ci gaba da kutsa kai zuwa Kudanci, tsakanin kilomita 3.5 zuwa Al-Bab, a cewar kungiyar mai sa ido.
Yayin da dakarun Turkiya da kuma 'yan tawayen suke tunkarar yankin ta arewaci, su kuwa na dakarun Syria suna kutsa kai ne ta gabashi da kuma yammacin yankin.
Duk wadannan kungiyoyin na yaki ne don korar mayakan kungiyar Da'esh amma abinda zai faru idan aka kori 'yan tawayen daga yankin na Al-Bab shine abinda babu masaniya akai.
Ita dai gwamnatin Turkiya na yi wa mayakan Kurdawa na Syria kallon kawaye ga jam'iyar Kuradwa ta PKK, wacce ta jima ta na kai hare-hare a kudu maso gabashin kasar ta Turkiyya.