‘Yantawayen kasar Libya na can suna neman milyoyin daloli daga jagabannin kasashen dake halartar taron da ake gudanarwa a Haddadiyar Daular Larabawa don shata makomar Libya bayan an kaswarda shugabanta na yanzu, Muammar Ghadafi.
‘Yantawayen kasar Libya na can suna neman milyoyin daloli daga jagabannin kasashen dake halartar taron da ake gudanarwa a Haddadiyar Daular Larabawa don shata makomar Libya bayan an kawarda shugabanta na yanzu, Muammar Ghadafi.
A wajen wannan taron da ake a birnin Abu Dhabi, kasar Italiya, wacce tayi wa Libya mulkin mallaka, tayi alkawarin bada tarbaccen Dala milyan 600, koda yake tallafin zai hada da rance ga ‘yantawayen.
kampanin dillacin labaran Associated Press yace ita ma gwamnatin shugaba Obama na Amurka tayi alkawarin kara yawan tallafin agajin da take baiwa Libya din zuwa Dala milyan 26 da dubu 500. Sakatariyar Harakokin Wajen Amurka Hilary Clinton ta gayawa mahalarta taron cewa “kwannakin Ghadafi sun kare.”