‘Yan Tawayen Houthis Sun Sha Alwashin Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Don Nuna Goyon Bayan Falasdinawa

‘Yan Tawayen Houthis

Houthis na kasar Yemen da ke samun goyon bayan Iran, za su ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa na tekun Bahar Rum domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa muddin Isra'ila ta ci gaba da aikata laifuka a kansu, in ji shugabansu a ranar Alhamis.

Abdulmalik al-Houthi ya fada a wani jawabi da ya yi ta gidan telebijin cewa "Ayyukanmu na da matukar tasiri ga makiya kuma mun samu babban nasara."

Ya ce kungiyar za ta ci gaba da tallafa wa Falasdinawa duk da hare-haren da Amurka da Burtaniya ke kai wa kan mayakan Houthin a Yemen a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da Houthi ke kaiwa kan jiragen ruwa na kasa da kasa a tekun Bahar Rum.

Hare-haren na Bahar Rum dai sun kawo cikas ga jigilar kayayyaki a duniya tare da tilasta wa kamfanoni sake hanya mai tsawo da kuma tsada a kudancin Afirka, kuma ya haifar da fargaban cewa yakin Isra'ila da Hamas na iya yaduwa tare da hargitsa Gabas ta Tsakiya.

~ REUTERS